DALILIN YIN AURE

ME YA SA ZAN YI AURE?

WATCH VIDEOS

Wannan tambaya ne mai sauƙi amma akwai abubuwa a tattare da shi. Kamar yanda muka sani ne ko wane mutum baligi zai so a ce ya yi aure a lokacin da yake so. Wato ya shirya fara rayuwar aure. To amma yana da kyau mu gyara zukatan mu, mu hau layin musulunci.

1. ME YA SA ZAN YI AURE?: Ina son na yi aure ne domin Allah (SWT) Ya halatta aure a tsakanin mu ƴan adam. Kuma sunnah ne na dukkan Annabawan Sa. Ibada ne wanda in na yi shi da kyau zai kai ni ga rahamar Allah. In kuma na kauce zai mun azaba. Hanya ne na samun garaɓasa masu yawan gaske, wanda za su kai mutum Jannah kuma su ɗaga darajarsa.

Ina son na yi aure saboda shi ne cikan kamalar mace ko namiji. Kuma ina son na samu jin daɗin duniya wanda aure yana a layin farko. Ina son in kare kai na daga wasu zunubai, misali zina, da haihuwan ƴaƴa ba a cikin aure ba. Wato in da zan sauke sha'awata a duk lokacin da ta taso mun cikin kwanciyar hankali, kuma babu tsoro ko fargaba. Ina son in yi aure domin in samu ƴaƴa wadanda jin dadi ne su a rayuwar mutum. In tarbiyyantar da su ta hanyar yiwa musulunci hidima. Da ma wasu abubuwa wanda mai yi ya san su, da dalilansa.

A wani ɓangaren kuma, wani zai yi aure ne domin kawai kada duniya ta ce yana yawon banza yaƙi aure. Wasu za su yi ne domin rufe wani zunubi na su, wasu zasu yi don mallake abokin zama ya zama bawa. Wani zai yi ne don kawai ya ga ya mallaki wata yana juya ta, yana nuna isa da shugabanci. Wani don ya samu abun duniya, kowa dai da na shi.

2. NIYYA: Ƴan'uwana kun san menene niyya, da kuma muhimmancin yin mai kyau a cikin aikin mutum. Niyya kyakykyawa ya kan raunana son zuciya ya ƙarfafa yi don Allah. Kuma yana ragewa zuciya shahawowi marasa amfani. Allah a kullum niyyar bawa Ya ke kallo, idan Ya ga kyakykyawan niyyarsa sai Ya ƙarfafa masa abun. Kuma Ya kawo masa shi da alkhairi fiye da yanda bai zata ba. In kuma Ya ga sharri da son zuciya sai Ya bar sa da ita. Sau da yawa ma'aurata su kan kuskure wajen niyya, a gaskiya yanzu niyyoyin mutane akan aure rabin su ba alkhairi bane. Kuma mu kan nesantar da musulunci da abubuwan da ya kawo mana a lokacin da muka so yin aure. Dole ka ɗauki niyya mai kyau, ka tsarkake zuciyarka yayin neman abokin zama ko yayin da zaka yi aure.

3. ADDU'A: Addu'a wajibi ce, domin Annabi (SAW) ya kwaɗaitar da sahabbansa akan yin istikhara wato neman zaɓin Allah a cikin dukkan komai. Idan mutum bai riga da ya samu abokin rayuwa ba nema yake yi sai ya rinƙa addu'a ta alkhairi. Ko da kuwa ya ɗan saka son zuciyar sa na Allah Ya hada shi da abokin zaman sa. Annabi (SAW) ya san da shahawowin zuciya shi ya sa a zaɓen mace ma ya jero dukiya, kyau, nasaba da addini a karshe. In muka tashi addu'a sai mu saka abin da ya dace a sama mu sanya son zuciya a ƙasa. Ma'ana ka/ki ce: Yaa Allah Ka haɗa ni da abokin rayuwa mai addini da tarbiyya. Mai halaye na gari, mai ilimin addini da na zamani dai dai gwargwado. Wanda zamu daidaitu da shi a cikin zamantakewar aure. Sannan Allah mai kyau, ko mai farare bugun Abuja, wanda zan ji daɗi in sha farfesu a gidansa. Ya kai ni hajj da Umura duk shekara. 😂 In kun duba zaku ga ka saka Allah a kashi 80 sai ka sa son zuciyarka kashi 20. To abu mai wuya son zuciyarka ya iya rinjayen kashi tamanin ɗinnan. Ko da mutum bai samu kashi 10 na son ransa ba sai yayi haƙuri domin Allah Ya sa a farko. To haka a ke son mace ko namiji su tsaya tsayin daka akan ra'ayoyin kirki, da niyya mai kyau yayin zaɓen abokin zama.

4. ISTIKHARA: Istikhara zai fara ne yayin da ka haɗu ko kika samu wanda kuka daidaitu. Wato kun samu fahimta a ra'ayi, kun fahimci banbance-banbancen ku da yanda zaku magance su. To sai kuma a ɗauki damarar istikhara, domin Allah (SWT) Ya faɗa mana sau da yawa zamu yi ta son abu, muna ɗauka shine alkhairi ko shi ya dace alhali sharri ne. Kuma zamu ji bama son abu, bamu damu da abun ba alhalin shine mafi alkhairi. Allah Ya ce Shi Ya sani alhalin mu bamu sani ba. Kenan mai hankali shi zai mayar da komai nasa wurin Masani. Sai Ya zaɓa masa abun da ya dace da rayuwarsa.

ADDU'AR ISTIKHARA: Jabir ibn Abdullah da Maihaifinsa (RAA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya kasance yana koya mana yin Istikhara (neman zaɓin Allah) a cikin dukkanin al'amura kamar yanda ya ke koya mana sura daga cikin surorin Alqur'ani. Ya kan ce: "Idan ɗayan ku yayi niyyar yin wani al'amari to yayi sallah raka'a biyu ba farillah ba sannan ya ce:

((ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﺳﺘﺨﻴﺮﻙ ﺑﻌﻠﻤﻚ، ﻭﺃﺳﺘﻘﺪﺭﻙ ﺑﻘﺪﺭﺗﻚ، ﻭﺃﺳﺄﻟﻚ ﻣﻦ ﻓﻀﻠﻚ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ، ﻓﺈﻧﻚ ﺗﻘﺪﺭ ﻭﻻ ﺃﻗﺪﺭ، ﻭﺗﻌﻠﻢ ﻭﻻ ﺃﻋﻠﻢ، ﻭﺃﻧﺖ ﻋﻼﻡ ﺍﻟﻐﻴﻮﺏ. ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻥ ﻛﻨﺖ ﺗﻌﻠﻢ ﺃﻥ ﻫﺬﺍ ﺍﻷﻣﺮ ) ﻭﻳﺴﻤﻲ ﺣﺎﺟﺘﻪ( ﺧﻴﺮ ﻟﻲ ﻓﻲ ﺩﻳﻨﻲ ﻭﻣﻌﺎﺷﻲ ﻭﻋﺎﻗﺒﺔ ﺃﻣﺮﻱ، ﻓﺎﻗﺪﺭﻩ ﻟﻲ ﻭﻳﺴﺮﻩ ﻟﻲ ﺛﻢ ﺑﺎﺭﻙ ﻟﻲ ﻓﻴﻪ، ﻭﺇﻥ ﻛﻨﺖ ﺗﻌﻠﻢ ﺃﻥ ﻫﺬﺍ ﺍﻷﻣﺮ ﺷﺮ ﻟﻲ ﻓﻲ ﺩﻳﻨﻲ ﻭﻣﻌﺎﺷﻲ ﻭﻋﺎﻗﺒﺔ ﺃﻣﺮﻱ، ﻓﺎﺻﺮﻓﻪ ﻋﻨﻲ ﻭﺍﺻﺮﻓﻨﻲ ﻋﻨﻪ ﻭﺍﻗﺪﺭ ﻟﻲ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﺛﻢ ﺭﺿﻨﻲ ﺑﻪ)). [ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻋﻦ ﺟﺎﺑﺮ ﻣﺮﻓﻮﻋﺎ].

"Ya Ubangijina! ina neman zaɓinka da iliminKa, ina neman tabbatuwar ikonKa, ina roƙon falalarKa Mai garma, Kai ke da iko ni ban da shi, Kai ne Masani ni ban san (komai ba) Kai ne masanin abin da yake ɓoye. Ya Ubangiji na! In Kana ganin wannan abu (sai ka faɗi abin da kake istikharan a kai) shi ya fi min a addinina da rayuwata da ƙarshen lamarina, to Ka tabbatar min da shi. Ka sauƙaƙe min sannan Ka yi min albarka a cikinsa. In kuwa Kana ganin wannan abu sharri ne gare ni a addin ina da rayuwata, da ƙarshen lamarina, Ka juyar da shi daga gare ni. Ni ma Ka juyar da ni daga gare shi. Ka ƙudurtar min da alkhairi sannan ka amintar min da shi" [Bukhari].

Duk wanda ya nemi zaɓin Mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma ya yi azama a cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba In sha Allah. Domin Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: "Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka ƙuduri aniya, to ka dogara ga Allah". Ba mafarki a ke yi ba kamar yanda mutane da yawa suka ɗauka. Ana ganewa ne da yanayin nutsuwar zuciya, idan aure ne sai ka ji zuciyar ka ya ƙara nutsuwa da yarinyar kuma ya karkata gareta. Haka ke ma zaki ji wani irin nutsuwa da baki da iko a kanta, kuma zuciyarki babu waswasin komai ko tsoro. Za a iya yin wannan sallah raka'a biyu da rana, ba dole sai da daddare ba. Sannan a yi ta yi ne sosai har sai an sami biyan buƙata.
Allah Ya sa mu dace.

WATCH VIDEOS

No comments:

Post a Comment